Zanga zanga mafi girma a Birtaniya
November 30, 2011A Birtaniya kimanin mutane miliyan biyu ne ma'aikatan sufuri suka shiga yajin aikin gama gari na kwana guda domin baiyana adawa da matakan tsimi da gwamnatin ta baiyana wanda ya hada da shirin rage kudaden fansho. Yajin aikin na daya daga cikin mafi girma da aka gani a Birtaniya tun tsawon shekaru 30 da suka gabata. Malaman makaranta da ma'aikatan jinya da jami'an shige da fice na daga cikin wadanda suka shiga maci da kuma zanga zangar lumana a fadin kasar. Ba'a dai sami jinkiri ba a filin jirgin saman Heathrow kasancewar an sami ma'ikatan shige da fice da dama da suka je wurin aiki. Firaministan Birtaniyan David Cameron ya baiyana zanga zangar a matsayin fargar jaji yana mai cewa garanbawul a fannin harkokin Fansho na ma'aikatan gwamnati abu ne da ya zama wajibi.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasir Awal