1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a ƙasar Yemen

February 15, 2011

Fito-na-fito a tsakanin magoya bayan gwamnatin Yemen da masu adawa da ita

https://p.dw.com/p/10HbN
Zanga-zangar adawa da gwamnatin Yemen.Hoto: picture alliance/dpa

Ɗaruruwan masu jerin gwanon nuna adawa da kuma masu goyon bayan shugaban ƙasar Yemen Ali Abdallah Saleh sun yi taho mu gama a Sana'a, babban birnin ƙasar Yemen. Rikicin dai ya ɓarke ne sa'ilin da jami'an 'yan sanda suka hana ɗaruruwan masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatin yin jerin gwanon su zuwa fadar shugaban ƙasar.

A lokacin da masu zanga zangar suka bar wurin ne kuma suka haɗu da masu nuna goyon bayan su ga gwamnatin, inda kowane ɓangare ya yi ta jifar ɗan uwansa da duwatsu.Jami'an 'yan sanda dai sun shiga tsakanin domin kwantar da rikicin.

Masu zanga zangar sun ɗauki tsawon kwanaki biyar a jere suna gudanar da zanga zangar neman shugaban ƙasar Ali Abdallah Saleh ya sauka daga mulki. Shugaban, wanda ke gadon mulki tun kimanin shekaru 30 kenan, ya bayyana cewar bashi da wata sha'awar neman sake tsayawa takara a zaɓukan ƙasar da za su gudana a shekara ta 2013.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu