Zanga-zanga a Yemen
May 9, 2011Talla
' Yan sandar ƙwantar da tarzoma a ƙasar Yemen sun yi amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla da kuma harsashen gaske domin tarwatsa masu zanga zanga a garin Taez dake tazaran kilomita 250 daga kudancin Sanaa babban birnin ƙasar.Majiyoyin jami'an kiwon lafiya sun ce mutun ɗaya ya rasa ran sa wanda aka harba da bindiga a lokacin zanga zangar da aka gudanar yayin da wasu gomai suka jikata.
Daman a jajibirin wannan yamutsi wasu mutane biyu sn mutu a lokacin wani zaman durshin da malaman makaranta suka yi a gaban gini ofishin ministan illimi.
Masu yin borai a ƙasar ta Yemen na ƙara matsa ƙaimi a yan ƙwanakin baya baya nan ga gwmnatin Ali Abdallah saleh da ta yi marabus.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza sadissou Madobi