Zanga-zanga a Girka saboda shirin tsuke bakin aljihu
May 8, 2016Talla
Shirin ya tanadi ƙara kuɗaɗen haraji da zabtare kuɗaɗen fansho da kuma korar wasu dubban ma'aikatan daga bakin aiki. Ana sa rai majalisar dokokin ƙasar za ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da wani daftarin ƙudirin a yau Lahadi a kan shirin, duk kuwa da matsin lambar da ƙungiyoyin ƙwadagon ke yi wa gwamnatin.
Hukumomin ba da lamuni na duniya su ne suka tilasta wa Girka yin wadannan sauye-sauye gabanin samun ƙarin rance domin tada komaɗar tattalin arzikinta.