1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Tsoron yaki tsakanin Isra'ila da Hezbollah

Abdullahi Tanko Bala SB
June 20, 2024

Yayin da rikici ke karawa kan iyakar Israila da Lebanon, kimanin mutane 150,000 tashin hankalin ya raba da muhallansu. Kana Israila ta sanya sojoji cikin shiri dangane da wani faifan bidiyon leken asiri na Hezbollah.

https://p.dw.com/p/4hJvv
Zaman tankiya kan iyakar Lebanon da Isra'ila
Zaman tankiya kan iyakar Lebanon da Isra'ilaHoto: Rebecca Ritters/DW

 

A wannan makon Israila ta sanya sojojinta cikin shirin ko ta kwana bayan da Hezbollah ta wallafa wani faifan bidiyo na leken asiri da ta yi ikrarin ta dauka na cibiyoyin sojin Israila da kuma wasu muhimman cibiyoyin farar hula ciki har da birnin Haifa mai tashar jirajen ruwa. Ministan harkokin wajen Isra'ila Israel Katz ya yi kashedi ga Hezbollah cewa za ta fuskanci kaskanci idan yaki ya barke gadan gadan a kan iyakar Israila da Lebanon. Tun a farkon wannan watan dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ruwaito cewa Israila ta harba farin garin hodar sinarin Phosphorous mai guba a kan garuruwan Lebanon, abin da ya saba dokokin kasa da kasa. Haka kuma a makon dai da ya gabata, Hezbollah ta harba rokoki fiye da 160 zuwa cikin Israila domin daukar fansa kan kisan kwamandojinta biyu.

Karin Bayani: Gaza zai iya ruruta rikicin Isra'ila da Hezbollah

Libanon I Zaman tankiya kan iyakar Lebanon da Isra'ila
Zaman tankiya kan iyakar Lebanon da Isra'ilaHoto: Hassan Fneich/AFP

Tun dai daga harin 7 ga watan oktoban 2023 da mayakan Hamas suka kai a kudancin Israila wanda ya hallaka mutane kimanin 1,200 al'amura suka tabarbare a kan iyakar Israila da Lebanon. Hezbollah kungiya mai karfi ta Falasdinawa wadda ke taka muhimmiyar rawa a al'amuran siyasa da na rayuwar al'umma a Lebanon ta dauki Hamas a matsayin kawa sannan kuma kasar Israila a matsayin abokiyar gaba.

Bayan yake-yake biyu na 1996 da na 2006 wadanda ba su kai ga gaci ba, Jami'an tsaron Isra'ila da Hezbollah suka zabi yin fito-na-fito da juna a yankunan kowannensu tare da samun hasara mai yawa. Dubban fararen hula, 'yan Lebanon kimanin 100,000 da 'yan Israila 60,000 da suke zaune a kan iyakoki, yakin ya sha raba su da muhallansu. Ana dai kara samun damuwa cewa rikicin da ke ruruwa a kan iyakar ka iya habaka zuwa gagarumin yaki. Wasu yan siyasar Israila masu tsattsauran ra'ayi na cewa ya kamata Israila ta kai wa Hizbullah hari a yanzu. Hasali ma wani binciken jin ra'ayi da aka gudanar a wannan watan ya nuna yawancin 'yan Israila suna ganin kaddamar da yaki a kan Hezbollah abu ne da ya dace.

Libanon I Beirut I Birnin Beirut na Lebanon daga sama
Birnin Beirut na Lebanon daga samaHoto: Elisa Gestri/Sipa USA/picture alliance

Sai dai wata cibiyar nazarin dabaru da ke da mazauninta a Washington a wani bayani da ta fitar a watan Maris ta ce harin 7 ga watan Oktoba ya kara jefa Israila cikin barazanar tsaro. Sai dai cibiyar ta ce Idan Hamas wadda ba ta da makamai da kuma horo kamar Hezbollah ta iya hallaka yan Israila 1,100 to kuma yaya Hezbollah wadda ta ke karfi da gogewa?

Babu dai tabbas ko gagarumin yaki zai barke. Kokarin diflomasiyya na kasa da kasa da ake yi a yanzu yana da nufin ganin an kare aukuwar hakan kuma kwararru da dama suna ganin ba dabara ba ce Isra'ila ta sake ballo da wani fagen daga a yayin da ta ke ci gaba da yaki a Gaza. Sun kuma nuna cewa Hezbollah tana da karbida makamai fiye da Hamas a Gaza. Ga Lebanon kuwa, kasar na fama da matsalolin siyasa da na tattalin arziki tsawon shekaru a yanzu. Hatta jam'ar kasar suna tausaya wa Falasdinawa inda aka kashe fiye da mutum 37,000 a Gaza a watanni takwas da suka wuce.