1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi: Mutuwar shugaban "Mutu ka Raba"

June 10, 2020

Al'ummar kasar Burundi na cikin alhinin mutuwar shugaban kasarsu da ke shirin barin gado Pierre Nkurunziza. Marigayin dai ya mutu yana da shekaru 56 bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ya yi.

https://p.dw.com/p/3dZxm
Präsident Burundis Pierre Nkurunziza
Marigayi shugaban kasar Burundi mai barin gado, Pierre NkurunzizaHoto: Reuters/E. Ngendakumana

An haifi marigayin ne a shekara ta 1963, mahaifiyarsa yar kabilar Tutsi ce yayin da mahaifinsa ya kasance daga kabilar Hutu. Rikicin kabilanci na shekara ta 1972 ne yai ajalin mahaifinsa. Bayan kammala digirinsa na farko, ya fara aikin malanta a jami'a. A shekarar 1995, bayan tsallake rijiya da baya a wani mumunan hari da aka kai musu a yakin basasa, ya shiga kungiyar 'yan kabilar Hutu har ya kai ga rike shugabancinta. A shekarar 2005 ya zama shugaban kasar Burundi, inda ya fuskanci kalubalen daidaita kasar da yaki ya daidaita.

Nkrunziza shugaban "Mutu Ka Raba"?

Labarin mutuwar Nkurunziza na zuwa ne makwanni kalilan kafin ya mika mulki ga sabon zababben shugaban kasar da zai gaje shi Évariste Ndayishimiye. A wannan lokaci da rai ya yi halinsa, masana na duba irin gwagwarmayar da ya yi ta daidaita al'amuran kasar kamar yadda Thierry Vircoulon da ke zama shugaban kungiyar samar da zaman lafiya ta kasa da kasa ya ke cewa: "Marigayin ya tsinci kansa ne a tsakiyar rigingimun kabilanci, kuma a matsayinsa na tsohon shugaban 'yan tawayen kabilar Hutu da ma irin rawar da ya taka a yakin kasar, ya samu damar shigewa fadar gwamnati."
Marigayi Nkurunziza ya kwashe shekaru 15 yana mulkar 'yar mitsitsiyar kasar da ke tsakiyar Afirka, to sai dai duk da ire-iren kalubalen da ya fuskanta wajen kawo daidaito da zaman lafiya tsakanin manyan kabilun kasar biyu da janyewa da ya yi daga tsayawa takara a karo na hudu, masu sharhi kan al'amura na cewa mutuwarsa ta bazata, tazo ne a daidai lokacin da ake tunanin ba zai bar sabon shugaban ya yi rawar gaban hantsi ba, ganin cewar ya nuna alamun son ci gaba da mulki.

Burundi Evariste Ndayishimiye zum Sieger der Präsidentenwahl erklärt
Sabon zababben shugaban kasar Burundi Evariste NdayishimiyeHoto: AFP

Matasa na son a samo mafita

Gwamnatin Nkurunziza dai ta yi kaurin suna wajen kame masu adawa da ita. yanzu haka wasu daga cikin 'yan kasar na ganin cewa duk da Nkurunziza ba ya raye, matsalar ba za ta sauya zani ba, domin kuwa jamiyyarsa da kuma wanda ya zaba a matsayin wanda zai gaje shi ne za su dare kan karagar mulkin. Marguerite Barankitse wani matshi ne da ya kafa wata kungiya da matasa da ma 'yan gudun hijirar Burundi ke samu suna tattauna lamuran kasar: "Muna jiran adalci, amma da alama zai yi wuya a yanzu, kasancewar matsalar na tattare da  jamiyya mai mulki ta CNDD-FDD ne. Yanzu a bayyane take karara, ana bukatar tattaunawa a siyasance domin lalubo hanyar warware matsalar kasar nan."

An dai kebe mako guda domin zaman makoki a Butrundin. Kana abin jira a gani shi ne ko jamiyya mai mulkin za ta amince da tattaunawar da matasan kasar ke bukatar a yi.