Zaman majalisar Palasdinu a Gaza
October 6, 2014A wata sanarwa da ministan ayyuka Ma'mon Abu Shahla ya fitar da aka rabawa manema labarai, ya ce Firaminsta da baki dayan minstocinsa za su hadu a yankin na Zirin Gaza domin tattaunawa cikin wannan mako. Sai dai ya ce kawo yanzu basu da tabbacin cewa ko gwamnatin Isra'ila za ta amincewa minstoci daga yankin Gabar Yamma da Kogin Jodan su zo Gazan domin halartar wannan taro ganin cewa tun bayan kafa gwamnatin minstoci daga yankin Zirin gaza na shiga taron majalisar zartaswar kasar ne ta hanyar yin amfani da sakon faifan Vedeo. Tun dai a watan Yunin da ya gabata ne bangarorin Palasdinawa na Fatah da Hamas suka amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa domin magance matsalolin da ke addabar Palasdinawa baki daya, matakin da Isra'ila ba ta yi maraba da shi ba.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo