1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na uku a taron kafa gwanatin kawance tsakanin CDU, CSU da SPD

Mohammad Nasiru AwalOctober 5, 2005

A gobe alhamis shugabannin dukkan jam´iyun da abin ya shafa zasu yi wani taro na musamman a Berlin

https://p.dw.com/p/BvZ9

Bayan taron dai wanda suka shafe sa´o´i biyu suna yi jam´iyun CDU da CSU da kuma SPD a daya bangaren sun ce sun samu ci-gaba a dangane da batun kulla babban kawance. To sai a dangane da batun shugaban gwamnati da ake takaddama akai, sassan biyu sun ce warware wannan cece-kuce a wani taron na musamman da shugabannin jam´iyun 3 wato CDU, CSU da kuma SPD zasu gudanar a gobe alhamis da yamma. Wannan taro dai zai samu halarcin ´yar takarar CDU Angela Merkel da shugaban CSU Edmund Stoiber da takwaransa na SPD Franz Müntefering da kuma shugaban gwamnati Gerhard Schröder.

A cikin sanarwar bayan taron na yau wanda shi ne na uku da sassan suka gudanar tun bayan zaben majalisar dokoki ta Bundestag a ranar 18 ga watan satumba, Schröder yace ba zai zama kadangaren bakin tulu a shirye-shiryen kafa kawancen ba. Sannan sai ya kara da cewa:

“Na yi imanin cewa yanzu jam´iyun Christian Union sun fahimci cewar dole ne shiga wannan taro bisa manufar tattauna batutuwa masu muhimmanci a dangane da kafa kawance.”

Schröder ya ce taron na yau yayi armashi kuma ya samar da kwakwaran ginshiki dangane da kafa wani babban kawancen.

Ita ma shugabar jam´yiar CDU kuma wadda ta kalubalanci Schröder a zaben ´yan majalisar dokokin Angela Merkel ta nuna gamsuwa da taron na yau da cewa ya nunar a fili irin halin da kasar ke ciki kuma manufar dukkan sassan biyu guda daya ce wato samar da wani yanayi mafi dacewa wajen kulla kawancen.

“A nawa gani ita ma jam´iyar social democrat a gaske ta ke wajen ganin kwancin wannan batu na kafa gwamnatin kawance da Christian Union. Ina fata taron shugabannin jam´iyun da za mu gudanar gobe za mu samun sukunin yin shawarwari bisa manufa. Kuma ina kyautata zato zamu samu tudun dafawa.”

Shi ma shugaban SPD Franz Müntefering ya nuna gamsuwa da taron na yau, inda ya ce jam´iyarsa ta kuduri aniyar kafa gwamnati ta ´yan sabon jini mai nuna adalci ga kowa da kowa.

Shi ma a nasa bangaren shugaban CSU kuma firimiyan jihar Bavariya Edmund Stoiber cewa yayi manufar su ta magance mawuyacin hali da ake ciki a kasuwar kwadago ta kasa da koma bayan tattalin arziki ta samar da wani ginshiki na yin shawarwari don kaiwa ga tudun mun tsira.

A karshe dai ra´ayin dukkan mahalarta taron na yau ya zo daya cewa daga cikin batutuwan da zasu tattauna a taron su na gobe zasu hada har da fasalin da kuma irin aikin da majalisar ministocin da za´a kafa nan gaba zata yi.