Zaben tsakiyar wa'adi a kasar Amirka
November 7, 2022A wannan zaben akan zabi dukkan 'yan majalisar wakilai, da kashi daya bisa uku na majalisar dattawa da kuma mukaman shugabancin jihohi da dama. Shekaru hudu baya a zaben tsakiyar wa'adi karkashin tsohon Shugaba Donald Trump, adadin alkaluma ya karu zuwa kashi 53.4 cikin dari.
A bana dai Amirka kasa ce mai daukar hankali a kan siyasar cikin gida. Martanin da kotun kolin kasar ta yi na soke dokar hana zubar da ciki, wanda ya tabbatar da 'yancin zubar da ciki a fadin kasar wata alama ce da ke nuna cewa siyasar kasar na da matukar bambanci tsakanin jam'iyyu da shugabanni. Masu sassaucin ra'ayi sun firgita da abin da suke gani a matsayin wani hakki na asali da aka kwace. Yayin da su kuwa masu ra'ayin mazan jiya suka yi murna da hukuncin a matsayin babbar nasara.
Abin kallo dai a wannan zaben shi ne makomar tsohon shugaban kasar Donald Trump. Ko magoya bayansa na iya samun nasara a banagaren sanatoci da majalisar wakilai da kuma a jihohi domin in hakan ya faru siyasar za ta shiga wani sabon babi, kamar yadda Jessica Taylor, 'yar jarida da ta kware a fannin majalisar Dattawa da gwamnoni ta fada.
A yanzu haka dai akwai 'yan takara da dama da ba su amince da halaccin gwamnatin Amirka mai ci ba, wadanda suke neman mukamai daban-daban. Lamarin da masana ke cewa shi ne yake kara kawo babban tunani a wannan zaben rabin wa'adi na Amirka. A bangaren sa shi ma Shugaba Joe Biden, wannan zaben shi ne babbar manuniyar karbuwarsa ga kasar ta Amirka.