Zaben shugaban kasa a Yemen
February 21, 2012A zaben sabon shugaban kasar da ke gudana wannan talatar a kasar Yemen, an shiga wani hali na adawa da zanga-zanga. A kudancin kasar kungiyar Al-kaida na kokarin yin kafar ungulu ga hadin kan da kasar ke kokarin ta cimma wajen yin zaben. Rahotanni sun ce a garin Mukalla, wasu masu dauke da makamai sun kai hari kan wani ofishin zabe, abunda ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in Soji ya kuma jikkata mutane biyu. A can a babban birnin kasar kuma Sana'a, ya kan dauki wani tsawon lokaci kafin wadanda suka cancanci yin zabe su kada kuri'ar su.
Da wannan zaben ne kasar ke fatar ganin karshen mulkin Ali Abdallah Saleh na tsawon shekaru 33. Mutun daya ne ke takarar neman kujerar mulkin kasar, wato mataimakin shugaban kasa Abd Rabbo Mansur Haddi. Ana sa ran idan har ya yi nasara, dan takarar mai shekaru 66 da haihuwa zai yi wa'adin shekaru biyu ne kacal akan kujerar mulki. To sai dai wadanda ke kudancin kasar sun sha alawashin kauracewa zaben.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal