1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango ta mamaye jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal YB
January 11, 2019

Jaridun Jamus sun fi mayar da hankali kan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda za mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a sharhin da ta rubuta ta fara da cewa sauyin madafun iko mai cike da tambayoyi.

https://p.dw.com/p/3BPxx
Kongo Kinshasa Felix Tshisekedi nach der Stimmabgabe
Hoto: Reuters/K. Katombe

Neue Zürcher Zeitung ta ce an bayyana dan takarar adawa Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Kwango, ko da yake abin a yaba ne, amma rahotannin da ke cewa gabanin a bayyana sakamakon zaben an tattauna tsakanin Shugaba mai barin gado Joseph Kabila da Tshisekedi game da sauyin madafun iko cikin ruwan sanyi. Ana kyautata zaton cewa akwai wani shiri da mutanen biyu suka yi idan Tshisekedi ya yi nasara ba zai sa a tuhumi Kabila ba.

Ita ma sharhinta kan kasar ta Kwango jaridar Die Tageszeitung ta ce zaben ka iya zama wata dama ta tarihi da za ta ciyar da nahiyar Afirka gaba. Ta ce matukar Felix Tshisekedi ya zama shugaban kasar Kwango watakila za a kawo karshen halin gaba kura baya siyaki da kasar ke ciki. Ta ce hakan zai zama karon farko da za a samu sauyin mulki cikin ruwan sanyi a tarihin kasar.

Tawaye na 'yan sa'o'i wannan shi ne taken rahoton da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta buga game da yunkuri  juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Gabon a ranar Litinin da ta gabata.

Gabun mutmaßlicher Putschversuch des Militärs
Jami'an tsaro sun bazu a Libreville bayan batun juyin mulkinHoto: Getty Images/AFP/S. Jordan

Jaridar ta ce wani gungun sojoji a Gabon sun afka wa kafar yada labarun kasar da ke Libreville babban birnin kasar inda suka  umarci sojoji da al'umar kasar da su yi tawaye saboda rashin gamsuwa da yadda lamura ke tafiya a kasar musamman yadda iyalin gidan Bongo suka mayar da mulkin kasar tamkar na gado ga shi kuma shi Shugaba Ali Bongo na fama da rashin lafiya.

Sudan Khartum Anhänger  Sadiq al-Mahdi  Opposition
Biranen Sudan na kara shiga zanga zangarHoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung da ta yi sharhi kan zanga-zangar da ta zama ruwan dare a Sudan tana mai cewa shugaban mulkin kama karya na Sudan Omar al-Bashir ya kasa gano hanyar magance jeri zanga-zangar adawa da gwamnatinsa a kasar, duk kuwa da rawar da ya sha kan dandamali a gaban magoya bayansa. Jaridar ta ce zanga-zangar da ta faro kan saboda tashin farashin biredi ta rikide zuwa neman shugaban ya sauka daga karagar mulki. Tun a shekarar 1989 Shugaba al-Bashir ya hau kan kujerar shugabancin kasar ta Sudan ya murkushe bore kala-kala da ya fuskanta a baya, sai dai a wannan karon matasa da ke jagorantar zanga-zangar na amfani da hanyoyin sadarwa na zamani don yin gangami kusan a kullum. Masu fafatukar kare hakin dan Adam sun ce matakan karfi da gwamnati ta dauka kan masu zanga-zangar sun yi sanadin rayukan mutum fiye da 40.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani