SiyasaTurkiyya
Za a zabi sabbin magadan gari a Turkiyya
March 29, 2024Talla
A cewar wani hasashe na jin ra'ayin jama'a, biranen Istanbul da Ankara za su ci gaba da kasancewa a hannun jam'iyyar 'yan adawa ta CHP, ta Social-Democrat. An yi hasashen cewar jam'iyya mai mulki ta AKP za ta samu koma baya a garuruwa da dama. Erdogan wanda ke kan karagar mulkin tun shekara ta 2003 ya bayyana a farkon watan Maris cewa, wadannan zabukan kananan hukumomi za su kasance zabukan karshe da aka shirya a karkashin ikonsa,