1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamnoni a jihohin Kaduna da Bauchi

April 28, 2011

Jihohi biyu na Kaduna da Bauchi sun biyo bayan sauran jihohin Nijeriya da suka yi zaben gwamnoni a farkon wannan mako, wanda shine ya kawo karshen zabubbuka a kasar a shekara ta 2011

https://p.dw.com/p/115vd
Kada kuri'a lokacin zabe a NijeriyaHoto: AP

A bayan jinkiri na yan kwanaki kalilan, masu zabe a jihohi biyu na arewacin Nijeriya, wato Kaduna da Bauchi ranar Alhamis sun sami damar kada kuri'un su, domin zaben sabbin gwamnonin da zasu shugabance su tsawon shekaru hudu masu zuwa. Ko da shike an gudanar da zabubbukan gwamnoni a sauran jihohin kasar, amma a wadnanan jihohi biyu an dage zaben, sakamakon tashin hankali da rikicin da suka biyo bayan kuri'un zaben shugaban kasa, inda yan adawa suka yi korafin magudi da rashin amincewa da sakamakon da aka samu.

Zaben na gwamnoni na ranar Alhamis, shi ya kawo karshen jerin zabubbuka da kasar ta Nijeriya ta fuskanta a watan April, abin da ya hada da zaben yan majalisun dokokin taraiya da na jihohi da zaben shugaban kasa da na gwamnoni. To sai dai kuma a yayin da Nijeriya suka kammala kada kuri'un nasu, yanzu dai hankali zai tattara ne ga kotunan shari'a na kasar, inda yan adawa da wadanda suka sha kaye a wadannan zabubbuka zasu shigar da kara domin neman abin da suke ganin zai zama hakki ne nasu.

Muna dauke da rahotanni a game da yadda zaben ya gudana a jihar Kaduna, inda wkailin mu, Ibrahima Yakubu ya duba mana sakamakon zaben da muhimancin sa a yanzu. Daga Bauchi kuma, wakilin mu, Ado Abdullahi Hazzad yayi mana nazarin yadda zasu zabe suka ynake hukunci a game da mutumin da zai shugabanci jihar su a matsayin gwamna har na wasu shekaru hudu masu zuwa, sa'annan wakilin mu a Abuja, Ubale Musa ya maida hankalin sa kan kalubalen da kotunan shari'a zasu fuskanta na sauraron kararrakin wadanda suka sha kaye ko wadanda basu ji da dadi ba a zabubbukan na Nijeriya da aka kammala a baya-bayan nan.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman