1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun hana mutane zabe

December 27, 2020

Yayin da 'yan adawa ke korafin matsalar tsaro a lokacin zaben kasar ta Afirka ta Tsakiya shugaban kasar Touadera ya ce komi na tafiya daidai.

https://p.dw.com/p/3nGSZ
ZAR Präsidentschaftswahlen, Wahllokal
Hoto: Alexis Huguet/AFP

Masu zabe a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kada kuri'unsu cikin firgici, yayin da ake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye.    

Tun da fari dai 'yan adawa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Francois Bozize, sun bukaci da a dakatar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a wannan Lahadi, har sai an samu cikakken zaman lafiya wanda kotun tsarin mulki ta yi watsi da kiraye-kirayen.

'Yan takara 16 maza 13, mata 3 ne ke zawarcin kujerar shugabancin kasar a yayin da sama da 'yan takara 1,500 suka tsaya takarar majalisar dokoki mai kujeru 140. 

Shugaba mai ci Faustin-Archange Touadera wanda ke neman wa'adi na biyu yayin da ya je kada kuri'a, ya ce akwai tsaro a rumfunan zabe. 

Sai dai  Anicent-Geoges Dologuele da ke takara a zaben ya bukaci da a yi waje da shugaba mai ci yana mai cewa
''Lokaci ya yi da zamu chanza gwamnati mai ci, mu tabbatar da cewa Touadera ba shi ba ne shugaban kasa ba gobe.''

Fiye da mutane miliyan daya da dubu dari takwas da sittin aka yi wa rajistar zabe, amma fiye da 'yan gudun hijira dubu dari biyar da chasa'in da takwas da ke a kasashe makwabta ba su samu damar kada kuri'a ba a cewar Majalisar Dinkin Duniya.