1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump da Kim Jong Un za su gana

Abdourahamane Hassane
May 10, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana ta shafinsa na Twitter cewar za su yi haduwa nan ta tarihi da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un a ranar 12 ga watan Yuni da ke tafe a Singapur.

https://p.dw.com/p/2xVMg
Kim Jong Un, Donald Trump
Hoto: picture alliance/AP Photo

Donald Trump ya ce da shi da takwaransa na Koriya ta Arewan za su saka damba ta farko don samar zaman lafiya a duniya. Wannan sanarwa ta zo ne awowi kalilan bayan Koriya ta Arewa ta sako wasu mutanen guda  uku 'yan Amirka da take tsare da su a kurkuku.