Za a shirya zaben gaba da wa'adi a Aljeriya
February 19, 2021Talla
Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya kuma ba da umurnin yin afuwa ga masu fafutukar nuna adawa da ke tsare bayan da ya rusa majalisar dokokin kasar. An dai kafa majalisar dokokin mai ci a yanzu ne tun a shekarar 2017 bisa wa'adi na shekaru 5 tare da shirya zabukan na 'yan majalisa a shekarar 2022.
Ko da yake shugaba Tebboune bai sanar da lokacin da za a gudanar da zaben ba , amma dai ana hasashen cewa wala'allah ya gudana tsakanin watan Juli da Satumbar wannan shekarar.
Shugaban na Aljeriya ya karfafa gwiwar matasan kasar kan su fito a dama da su wajen tsayawa takara tare da yin alkawarin biyan kudaden yakin neman zabensu.