1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila da Hamas sun lamunta a shigar da kayan agaji a Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou ZMA
January 17, 2024

Duk da tsananin luguden wutar da Isra'ila ke yi a yankin Zirin Gaza, hukumomin kasar da na Hamas sun amince da a shigar da kayayakin agaji ga mabukata a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4bLfB
Hoto: Ibraheem Abu Mustafa/REUTERS

Istra'ila ta kara tsananta luguden wutar da take yi a kudancin Zirin Gaza, a daidai lokacin da ake dakon shigar da kayayakin jin-kai musamman ma na magunguna ga mabukata, bayan da ta cimma wata yarjejeniya da Hamas karkashin jagorancin Katar da Faransa.

Karin Bayani :  Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun kasa da kasa

A wannan Laraba ake sa ran shigar da kayayakin agajin daga mashigar Masar zuwa Zirin Gaza, inda ake sa ran magungunan za su isa kai tsaye har ga Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su.

Karin Bayani :  Antony Blinken ya yi tozali da Mahmud Abbas kan rikicin Hamas da Isra'ila

Shaidun gani da ido sun tabbatar wa manema labarai cewar a daren da ya gabata, jiragen yakin Isra'ila sun yi barin wuta kusa da asibitin Nasser da ke Khan Younis, hare-haren da ma'ikatar lafiyar Gaza ta ce an kashe falasdinawa fiye da 80.