Za a sake yin shari'a Hosni Mubarak
January 13, 2013Kotun da ke karya shari'a ta amince ta sake duba ƙaran da Hosni Mubarak da kuma ministansa na cikin gida Habbib al Adli suka shigare a gabanta,na ta sake duba hukumcin da wata kotun ta yankema su na ɗaurin rai da rai.
Dangane da tuhumar da ake yi masu da hannu a kisan masu bore a lokacin juyin juya hali da aka yi a kasar a shekarun 2011. Wani dan jarida daga birni Alƙahira ya ce a yanzu sai an sake lallawa.
'Ggaskiya ne za a sake shari'ar a kan tuhumar da ake yi masu da kuma wani batun cin hancin na sayar da iskan gaz ga Isra'ila da tsohon shugaban ya yi."
A nan gaba na ne kotun za ta baiyana sunnan kotun da ta dace domin sake gudanar da shari'a ga Mubarak da tsohon ministansa na cikikn gida da kuma ya'yan sa guda biyu.Amma kafin lokacin za a cigaba da tsare shi a gidan waƙafi ,akan wani batun na kyautar kuɗi da ya karɓa daga wata jaridar mallakar gwamnatin ta Al haram a lokacin da ya ke yin mulki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal