Za a je zagaye na biyu a zaben Turkiyya
May 15, 2023A yanzu dai ta tabbata za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a Turkiyya a ranar 28 ga wannan watan na Mayu, za a fafata a tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdogan da babban mai kalubalantarsa Kemal Kiliçdaroglu.
Shugaba Erdogan na fuskantar matsin lamba duk da cewa kuri'u kadan yake nema ya sake darewa kan karagar mulkin da ya shafe shekaru 20 akai, alkaluman da Hukumar zaben CEC ta fitar na nuni da cewa, duk da kuri'un Turkawa mazauna kasashen ketare Erdogan na da kaso 49.3 cikin dari a yayin da babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu,ya sami kashi 45 cikin dari na kuri'un da aka kada
Tuni shugabanin kasashen duniya da suka hada da Amurka da Rasha suka baiyana fatan alkhairi da bayar da goyon bayansu ga zabin Turakawan da suka kada kuri'unsu a zaben na 2023. Shugabannin Kungiyar tarayyar Turai EU suma sun mika sakonsu na taya murna ga daukacin al'ummar Turkiyya kan yadda suka yi dafifi wajen fita zaben wanda zai jagoranci kasar a zagaye na farko, in da suka bayyana hakan a matsayin 'yanci na dimokaradiyya.
Manyan Jaridun Turkiyya sun yi ta sharhi kan batun zagaye na biyu na zaben, kasancewar Erdogan da babban abokin karawarsa Kemal Kilicdaroglu babu wanda ya samu kaso 50 cikin dari duk da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na cewa Erdogan zai iya kai labari.
Kilicdaroglu wanda ke jagorantar kawancen jam'iyyu 6 ya soki Erdogan, tare da zargin an tafka magudi wajen shigar da alkaluman sakamakon, sai dai ya yi kira ga magoya bayansa kimanin milyan 84 da su kwantar da hankali.
Sakamakon farko ya nuna cewa, jam'iyyar Erdogan ta AKP ta samu kuri'u 321 a kujerun Majalisar dokokin kasar ta Turkiyya, yayin da babbar jam'iyyar da ke kalubalantarsa ta sami kujeru 213 sai kuma kawancen jam'iyyun Kurdawa da ke da kujeru 66.
Kazalika wani kwararren kan ilmin tarihin Gabas ta tsakiya da kuma siyasa da ke Jami'ar St. Lawrence a birnin New York na Amurka Farfesa Howard Eissenstat ya ce, wannan sakamako zai bai wa Erdogan damar sake lashe zaben a zagaye na biyu da za a shiga, kasancewar al'ummar kasar ba sa bukatar rarrabuwar kai a al'amuran da suka shafi siyasar Kasar.