Za a fuskanci karancin cimaka a duniya
March 11, 2021Talla
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci tallafin dalar Amirka sama da miliyan biyar, domin ceto mutane miliyan talatin da hudu wadanda yaki ya daidaita daga afkawa cikin matsanacin karancin cimaka.
Wani kiyasi da aka yi a wajen taron kwamitin tsaro na Majalisar, na nuni da cewa kusan mutane miliyan tamanin da takwas ne ke fama da matsanaciyar yunwa a kasashen da ake yaki a fadin duniya, sai dai adadin ka iya dara na bara da kaso ashirin cikin dari a wannan shekarar ta 2021.
Kasashen da abin ya fi kamari sun hada da Yamen da Sudan ta Kudu da kuma Burkina Faso, kasashen da yanzu haka muatane sama da dubu dari da hamsin yunwar ta yi wa mugun ta'adi.