Kungiyar NATO ta ce dole ne a binciki Rasha
August 26, 2020Talla
A karon farko kungiyar tsaro ta NATO a ranar Larabar nan, ta bakin shugabanta Jens Stoltenberg ta ce babu makawa sai an gudanar da bincike dangane da gubar da aka sanya wa jagoran adawar kasar Rasha Alexei Navalny bayan da likitoci a Jamus suka tabbatar da cewa mutumin ya hadiyi guba.
Navalny da ke samun kulawa a wani asibiti a birnin Berlin na Jamus, ya kasance babban mai adawa da mulkin shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Hukumomin fadar Kremlin sun yi tsayin daka kan cewa binciken likitocin Jamus na cewa guba ce aka sanya wa madugun adawar, labarin kanzon kurege ne.