Za a daure tsohon shugaban kasar Peru
February 10, 2017Talla
Ana zargin tsohon shugaban da karbar cin hanci na dala miliyan 20 daga kamfanin aiyuka na kasar Brazil, kamfanin ya bada kudaden ne don a ba su damar gina babban titin da ya hada birnin Rio da Jenairo da kuma Lima. Masu gabatar da karar dai sun gabatar da shedu a gaban kotu da ke nuna almundahana da stohon shugaban ya aikata a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2006, a lokacin ya na kan karagar mulki sai dai bangaren Toledo sun ce za su daukaka kara.