1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓuɓɓukan gama gari a Tanzaniya

October 31, 2010

Ana kyautata zaton cewa shugaba mai ci yanzu Jakaya Kikwate zai sake samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar

https://p.dw.com/p/PuoG
Jakaya Kikwete, shugaban ƙasar TanzaniyaHoto: DW

A ƙasar Tanzaniya yanzu haka an buɗe runfunan kaɗa ƙuri'u a zaɓuɓɓukan gama gari da ake gudanarwa a ƙasar, wanda ake sa ran shugaba mai ci yanzu Jakaya Kikwate zai sake samun damar ɗarewa akan kujera ta shugabanci a wa'adi na biyu na shekaru biyar.Masu aiko da rahotannin sun ce an barbaza 'yan sanda ko'ina a runfunan zaɓe kimanin dubu hamsin da biyu domin lura da zaben. Jagoran 'yan adawa na ƙasar Chadema Wilibrod Slaa ya yi kira ga magoya bayansa da su bashi damar jarraba tsarinsa na yaƙi da cin hanci da kuma samar da ilimi da kiwon lafiya ga al 'uma.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas