1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen 'yan majalisa a ƙasar Birma

April 1, 2012

An ƙaddamar da zaɓen cike gurbi na 'yan majalisar dokoki a Birma inda ake sa ran fitacciyar 'yar adawan nan wadda ta sami lambar yabo ta Nobel Aung San Suu Kyi zata yi nasara.

https://p.dw.com/p/14W2L
Myanmar's pro-democracy leader Aung San Suu Kyi talks to supporters during a campaign stop in Pyar Pon township, Myanmar, Friday, Feb. 17, 2012. (AP Photo/Khin Maung Win)
Aung San Suu KyiHoto: AP

Waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a a ƙasar Bama sun fara zuwa runfunan zaɓe domin jefa ƙuri'unsu a zaɓen cike gurbin da aka fara da safiyar wannan lahadin. Ana sa ran wannan zaɓe zai kasance mafi adalci a cikin duk wadanda ƙasar ta taba gani na tsawon shekaru gommai yanzu.

Daga cikin 'yan takaran har da fitacciyar 'yar adawar nan Aung San Suu Kyi, wacce ke takarar wannan gurbi a karon farko. Duk da cewa an bata damar tsayawa takarar, mai lambar yabon ta Nobel ta riga ta yi zargin cewa za'a tabka maguɗi a zaɓen. Ita dai Suu Kyi mai shekaru 66 da haihuwa ta kasance a ƙarƙashin ɗaurin talala lokacin da aka yi zaɓukan ƙasar na shekarun 1990 da na 2010. Jamiyyarta ta National League for Democracy ta yi gagarumar nasara a zaɓen shekarar 1990. To sai dai dakarun sojin ƙasar ba su bar su sun kama aiki a hukumance ba.

Wannan zaɓe na ran lahadi, ya zo ne bayan da dakarun suka kawo ƙarshen mulkin sojin nasu a bara. Masu sanya ido sun yi ammanar cewa gwamnatin na so Suu Kyi ta sami kujera a majalisar dokokin kasar, domin haka zai nuna a zahiri cewar a shirye ta ke ta gudanar da sauye-sauye a fanin siyasarta domin baiwa ƙasashen yammaci ƙarfin guiwar sassauta takunkumin tattalin arzikin da suka ƙaƙaba wa ƙasar amma kuma sun ce basu da isashen lokaci kamar yadda wannan matar ta bayyana

"ta ce muna da kwana biyu ne kafin zabe dakuma kwana biyu bayan zabe saboda haka wannan lokaci ba zai ishe mu mu sanya ido yadda muke so ba"

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mouhamadou Awal