Yunwa na barazana a wasu kasashen duniya
August 9, 2017Kwamitin sulhun ya ce mutane fiye da miliyan 20 ne ke fuskantar barazana ta yunwa a kasashen Yemen, Somaliya, Sudan ta Kudu da kuma Arewa maso gabashin Najeriya, inda rikicin Boko Haram ya yi babban lahani. A sanarwar da membobisa 15 suka sa wa hannu, kwamitin sulhun ya yi Allah wadai da halin matsi da fararen hulla ke fuskanta a yankunan da ake fama da yake-yake, inda sanarwar ta kuma soki yadda rikice-rikicen ke hana ma'aikatan agaji shiga yankunan domin kai kayan agaji ga al'umma wanda akasari shi ne ke sanya lamarin ya na kara yin kamari.
Cikin sanarwar Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga dukannin bangarorin da ke yake-yake da su mutunta dokokin kasa da kasa na bai wa fararen hula kariya, da kuma kare duk wasu asibitoci da kayayyakin aiki na asibitoci da ma'aikatan kiwon lafiya don gudun fadawa cikin ire-iren wannan hali na tsaka mai wuya da al'umma ke shiga.