Kokarin neman sasanta rikicin jam'iyyar PDP
April 2, 2023Bayan share tsawo na lokaci cikin mummunan rikici, jam'iyyar PDP ta adawa ta dau hanyar sulhunta tsakanin 'ya'yanta, da ya zuwa yanzu ke lashe miki na rashi tare da cija yatsa kan rashi a zabukan kasar. PDP da ta share tsawo na lokaci cikin halin rudani, daga dukkan alamu na neman hanyar kai karshen rabuwar da ta kai ta ga faduwa a zabukan kasar.
A cikin jeri na matakan jam'iyyar na zaman janye dakatarwar da ta kai ga yi ga wasu tsofaffin gwamnoni da tun da farkon fari shugabancin Ayorchia Ayu ya kai ga yi bisa zagon kasa cikin harkokin jam'iyyar. A yayin kuma da ta tilasta reshen jihar Binuwe ya dakatar da shugabanni na mazabar Ayun da suka dauki matakin tsige Ayun a cikin makon da ya shude.
Sake komawar Ibrahim Shema ko bayan Ayo Fayoshe da ma uwa uba Anyim Pious Anyim a banagren mutanen Wike, da kuma rushe dakatarwar Ayun a bangare na Atiku Abubakar na kama da kokari na mai da wuka cikin kube na bangarorin jam'iyyar guda biyu, bangarorin da a baya suka dauki lokaci suna fafatawa, kuma suka kare kare-jini biri ma a haka yayin zaben.
To sai dai kuma in har 'yan lemar suna shirin da su dinke, bayan kai wa ya zuwa kirga asarar zaben, akwai tsoron asarar da ke shirin tasiri a shekarun da ke tafe, na neman zama fatalwa a tsakanin 'ya'yan da ke da fatan kare azumi na shekaru takwas.