Yiwuwar yin sulhu a kasar Yemen
September 11, 2015Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta shirya tataunawar sulhun wanda za a gudanar a mako mai zuwa a kasar Oman, domin kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Yemen din. Sai dai kakakin gwamnatin Yemen din Rajih Badi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa baya tsammanin tattaunawar za ta gudana kamar yadda aka tsara kasancewar har yanzu bangaren 'yan tawayen Houthi ba su ce uffan ba kan batun. A wannan Alhamis dai shugaban kasar ta Yemen Abedrabbo Mansour Hadi da shi ma ke gudun hijira a kasar Saudiyya ya gindaya janye war 'yan tawayen Houthi daga yankunan da suka mamaye tun a shekarar da ta gabata a matsayin sharadin zama kan teburin sulhun. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa sama da mutane 4,500 ne suka hallaka tun bayan da Saudiyya ta fara jagorantar rundunar taron dangi wajen yin luguden wuta a Yemen din cikin watan Maris din da ya gabata.