Yunkurin kasashen Turai na magance kin biyan haraji
April 13, 2013Talla
Shugaban hukumar tarayyyar Turai Herman van Rompuy ne ya shaida hakan a jiya Juma'a inda ya kara da cewar kasashen za su dauki wannan mataki ne a taron da za su yi cikin watan Mayu mai zuwa domin kuwa masu kin biyan haraji na jawowa nahiyar asarar kudin da yawasa ya kai yuro zambar miliyan guda a kowacce shekara.
Van Rumpoy ya ce taron zai yi amfani da wannan dama ce domin kawar da duk wata kariya ta siyasa da masu kin biyan haraji ke amfani da ita wajen aikata wannan laifi to sai dai kasashen irin su Austriya na kokarin turewa wannan yunkuri.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Muhammad Awal Balarabe