Yunkurin hana Rasha zuwa gasar birnin Rio de Janeiro
July 21, 2016Kotun kasa da kasa da ta saurari korafe-korafen wasanni a ranar Alhamis din nan ta yi watsi da daukaka karar 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Rasha wadanda ke neman kotu ta dauki mataki da zai hana haramta musu zuwa gasar wasanni a Brazil, abin da ke nuna akwai yiwuwar kwamitin da ke shirya wasannin na Olympic zai iya dakatar da Rasha daga halartar wasannin kasa da kasa na Olympic da za a yi a birnin Rio de Janeiro na Brazil, saboda zargin badakalar da ta shafi amfani da kwayoyi da ke sa kuzari a tsakanin 'yan wasa a lokutan wasanninsu na baya.
A ranar Lahadi kwamitin na IOC zai zauna inda a nan ne zai bayyana ko za a dakatar da kasar ta Rasha daga halartar wasannin na Rio de Janeiro a Brazil da za a fara daga ranar biyar ga watan Agusta mai zuwa ko kuma a'a.