Yunkuri wadata Afirka da makamashi
January 21, 2016Wannan kokari da masu ruwa da tsakin ke son yi dai na da nasaba da yadda nahiyar Afirka ta zamto kurar baya wajen samawa al'ummarta makamashi mai tsabta don gudanar aiyyukan yau da kullum. A tsarin dai, ana son ganin an yi amfani da wannan batu wajen ganin an bunkasa tattalin arzikin nahiyar. Da ya ke magana kan wannan batu yayin wani zama da su ka yi wanda yake bangare ne na taron na Davos da ke gudana, shugaban banki raya kasashen Afirka na ADB Akinwumi Adesina cewa ya yi Afirka fa ta gaji da zama cikin duhu.
"Afirka na fama da tarin kalubale na makamashi. Muna da mutanen da suka kai miliyan 645 da ba sa samun wutar lantarki wanda hakan ke jawowa nahiyar asara babba. Maganar dai kwaya daya ce, Afirka fa ta gaji da zama cikin duhu wannan ne ma ya sanya muka zabi daukar tsauraran matakai na kawo karshen matsalar."
Kaiwa ga cimma wannan buri da aka sanya a gaba ba abu ne mai yiwuwa ba kamar yadda masu sanya idanu kan batun na makashi a Afirka suka nunar. Da dama dai na aza ayar tambaya kan irin matakan da za a yi amfani da su wajen wadata daukacin nahiyar da makashi daga yanzu zuwa shekara ta 2025 kamar yadda ake fata. Kan haka ne shugaban ADB Akinwumi Adesina ya ce za su yi wa matsalar taron dangi don cimma burinsu kamar yadda aka yi a sauran nahiyoyi.
"Abu ne mai yiwuwa domin kuwa wasu sun yi. Matakan da za mu dauka wajen cimma hakan a wannan hadaka tamu su ne dukannin wanda ke harka ta makashi a Afirka za su kara yawan jarin da su ka sanya, na biyu kuwa shi ne kasashen da wannan matsala ta fi shafa za su rubanya kudin da suke sanyawa a makamashi da nufin ganin an samar da dala biliyan 50 a kowacce shekara sannan kuma za a yi kawance tsakanin gwamnatoci da 'yan kasuwa musamman ta bangare samar da karin kudi."
Masu ruwa da tsaki kan batun ciyar da Afirka gaba kamar tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan na daga cikin wanda ke kan gaba wajen jinjinawa wannan aiki har ma ya ke cewar in komai ya kammala, Afirka za ta taimaka wajen rage dumamar yanayi da yanzu haka ya addabi duniya.
"Idan muka yi aiki tare, muka kuma nemi kudin da za a zuba a aikin to za mu ci nasara. Idan aka samawa Afirka makamashi to muna bada gudumawa ce wajen rage dumamar yanayi domin kuwa za a koma amfani da makamashin da ake sabuntawa kuma ina ga Afirka za ta iya kansacewa kan gaba dangane da haka saboda yanayin da muke ciki."