Yuganda na shan suka kan dokar luwadi
May 30, 2023Talla
Shugaba Joe Biden na Amirka na daga cikin shugabanin kasashen Yamma da suka soki matakin da gwamnatin kasar Yuganda ta dauka na haramta mu'amalar jinsi daya a kasar, ya na mai cewa, hakan ya tauye hakkin dan adam. Wannan tsokacin shugaban ya kuma hada da barazanar katse tallafin da Amirka ke bai wa kasar tare da dakatar da zuba jari a kasar da ke yankin kahon Afirka.
A ranar Litinin (29.05.2023) ne, shugaban kasar ta Yuganda Yoweri Museveni ya rattaba hannu kan dokar da ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ko ma kisa kan duk wanda aka samu da laifin yin luwadi ko madigo a kasar, dokar da tuni ta janyo martani na suka daga kasashen Yamma.