1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar cirewa Rasha takunkumi

Ahmed SalisuJanuary 22, 2016

Amirka ta ce muddin aka kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya kan rikicin Ukraine to za a iya cirewa Rasha takunkumin da aka sanya mata nan da 'yan watannin da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1HifF
Petro Poroshenko Wladimir Putin Ukraine Russland Konflikt
Hoto: picture-alliance/dpa/Ch.Ena

Sakatare harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce akwai yiwuwar dage takunkumin da aka azawa Rasha in har aka cimma matsaya kan yarjejeniyar zaman lafiya a rikicin Ukraine.

Kerry ya ce ''na tattauna da mataimakin shugaban Amirka Joe Biden da kuma Shugaban Ukraine Petro Poroshenko kan yarjejeniyar Minsk. Ina ganin in har aka tashi tsaye kana aka cimma yarjejeniyar da za ta kawar da matsaloli da ke tsakanin bangarorin biyu to janyewa Moscow takunkumin da ke kanta abu ne da za a iya yi a 'yan watannin da ke tafe.''

A cikin shekarar 2015 da ta gabata ce dai aka cimma yarjejeniya kan rikicin Ukraine a birnin Minsk na kasar Belarus, inda shugabannin Faransa da Jamus da kuma Rasha da Ukrraine da ke rikici su ka amince da ita.