1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen za ta kawo karshen yaki a kasarta

February 5, 2021

Ministan harkokin wajen Yemen ya ce za su yi aiki tare da Amirka don kawo karshen yaki a kasar da tafi fuskantar matsalar talauci a daular larabawa.

https://p.dw.com/p/3owpE
Grenzsoldaten an der jemenitisch-saudischen Grenze
Hoto: picture-alliance/dpa/The Yemeni Army

Ahmed Awad Bin Mubarak ya jaddada cewa 'yan tawayen Houthi da masu marawa Iran baya ne ke zama babban cikas ga zaman lafiya da ke baiyana kariya ga shigar sojin Saudiyya Yemen.

A ranar Alhamis ce shugaba Biden na Amirka ya sanar da cewa zai kawo karshen goyon bayan kasarsa ga yakin da Saudiyya ke yi a Yemen. Rikicin da ya shafe shekaru biyar dai ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da dubu 1 da 30 wanda ke zama rikici mafi muni a duniya.

Ka zalika Shugaba Biden ya kara yin kira kan tsagaita wuta da bude hanyoyin isar da karin tallafi da kuma dawo da dadaddiyar tattaunawar zaman lafiya.