1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Yemen ya kazance

Ramatu Garba Baba
June 13, 2018

Rahotannin na cewa mayakan Hutsi ashirin da biyu ne suka halaka a sanadiyar luguden wuta da dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta suka kaddamar a kokarin karbe birnin Hodeida daga hannun mayakan Huthi.

https://p.dw.com/p/2zTuA
Jemen Feuer in Lagerhalle in Hodeida
Hoto: Reuters/A. Zeyad

Babbar tashar jiragen ruwan da ke birnin Hodeida na da matukar muhimmanci wajen shigar da kayan agaji a kasar wacce rikicin yaki ya daidaita. Ana kuma ganin mayakan na Huthi da ke rike da ikon wajen na anfani da ita wajen shigo da makaman da suke yakar gwamnatin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana matukar damuwa kan kazancewar rikicin na Yemen, duba da halin da dubban mutane ke ciki na bukatar taimakon kayyakin agaji a harin da ta ce na matukar barazana ga rayuwar fararen hula da ke zaune a yankin.