1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aiwatar da matakin tsagaita wuta a Yemen

Zainab Mohammed Abubakar
May 11, 2019

A matakin farko tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Sweden, 'yan tawayen Houthi na shirin janyewa daga tashoshin jiragen ruwa guda uku da ke karkashin ikonsu

https://p.dw.com/p/3IKcC
Jemen Hafenstadt Hudaida
Hoto: Getty Images/AFP/S. Al-Obeidi

Ana kyautata zaton janyewar 'yan tawayen da ya samu jinkiri tun daga watan Janairu, zai kammalu a ranar Talata mai zuwa a cewar shugaban kwamitin MDD da aka tura yankin Janar Michael Lollesgaad.


Dan asalin kasar Denmark, janar din ya yi maraba da wannan manufa ta 'yan tawayen da ke samun goyon bayan 'yan Shi'ar kasar Iran, na janyewa daga tashoshin jiragen ruwan na Hodeida, Saleef da Ras Issa

.
Janyewar wani bangare ne na yarjejeniyar da aka cimmawa a kasar Sweden a watan Decenban da ya gabata, da ake wa fatan wani gagarumin mataki na kawo karshen yakin na Yemen da ya yi sanadiyyyar dubban rayuka.