Yemen ta yi tayin sulhu ga 'yan tawaye
October 19, 2015Gwamnatin Shugaba Abd- Rabbo Mansour Hadi wanda ya tsere zuwa kasar Saudiyya tun bayan da 'yan tawayen kungiyar Huthis ta 'yan Shi'a suka kama babban birnin kasar Yemen ta ce a shirye take ta hau tebirin tattaunawa da 'yan tawayen kasar a karkashin jagorancin Majalissar Dinkin Duniya.
Kakakin shugaban kasar ta Yemen Rajeh Badi ne ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wannan aniya tasu, inda ya ce sun yi wannan tayin neman sulhu ne domin kawo karshen yakin da aka share watannin bakwai ana gwabzawa tsakanin sojojin da ke ci gaba da yin biyeyya ga Shugaba Abd-Rabbo Mansour Hadi da ke samun dafawar wasu kasashen Larabawa a karkashin jagorancin Saudiyya da kuma mayakan Kungiyar 'yan tawayen Shi'a ta Huthis.
Sai dai har kawo yanzu Majalissar Dinkin Duniya ba ta tabbatar da samun wannan tayi ba a hakumance daga hukumomin kasar ta Yemen ko kuma ma lokaci dama gurin da za a gudanar da tattaunawar.