1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen ta shiga mawuyacin hali

May 30, 2017

Ana kara gargadi kan mawuyacin halin rashin abinci a Yemen lokacin tattaunawar da aka yi a zauren kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2drh1
Yemen Sanaa - Menschenmengen bei Essensausgabe
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadi game da yaduwar cutar amai da gudawa da rashin abinci tsakanin milyoyin mutane a kasar Yemen, bayan kwashe shekaru biyu ana yakin basasa tsakanin bangaren gwamnati da 'yan tawayen Houthi.

Karamin-sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da jinkai Stephen Rothwell O'Bien ya ce kasar ta Yemen ta zama mafi karancin abinci a duniya, inda kusan mutane milyan bakwai suke daf da fadawa karancin abinci. Kuma ya fadi haka ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya lokaci wata muhawara. Karamin-sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da jinkai Stephen Rothwell O'Bien ya kuma ce babu fari a kasar ta Yemen amma yaki tsakanin bangarori masu rirkici da juna ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.