1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun kawance na cin galaba a Hodeidah

Abdul-raheem Hassan
June 16, 2018

Sojojin kawancen da Saudiyya ke jagoranta wadanda kuma ke samun goyon bayan sojojin gwamnati sun karbe iko da wasu yankunan birnin Hodeidah.

https://p.dw.com/p/2zfSN
Jemen Regierungstruppen starten Offensive zur Rückeroberung Hodeidas
Hoto: Getty Images/AFP/N. Hassan

A tsakiyar makon ne dakarun suka kaddamar da hare-hare kan 'yan tawayen Huthi a babbar tashar jirgin ruwa da ke kasar, bayan da wani harin 'yan tawaye a kudu da birnin Hodeida ya halaka sojoji 12. A yanzu dai sojoji na ci gaba da dannawa birnin tare da samun nasara kan 'yan tawayen da suka yi kaka gida da filin jirgin na Yemen.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan halin kunci da dubban fararen hula ke ciki, tun bayan da yankin ya fada hannun 'yan tawaye a shekarar 2014. Kwace birni zai zama nasara mafi girma ga sojojin kawancen.