Yemen na gab da tsunduma yakin basasa
March 23, 2015Majiyoyin tsaro sun ce 'yan tawayen Yemen sun tura karin dakaru zuwa yankin kudancin kasar bacin gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na cewa kasar na gab da tsunduma cikin wani yanayi na yakin basasa.
'Yan Houthin sun kara da kananan kabilun yankin kudancin wadanda mafi yawan su 'yan Sunni ne, lokacin da suke tinkarar birnin Aden, inda shugaba Abdurabbo Mansour Hadi ke samun mafaka tun bayan da ficce daga fadar gwamnati a watan jiya.
Ranar lahadi, 'yan Houthin dai sun anshe filin jirgin saman da ke kusa da sansanin sojin Taez. Wannan birni na Taez shi ne birni mafi girma a mataki na uku a kasar ta Yemen, kuma yana da tazarar kilometa 180 daga yankin arewacin birnin Aden, sannan bugu da kari ana masa kallon kafa ta shiga zuwa inda Mansour Hadi ke samun mafaka.