1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci taimaka wa kasar Yemen

Zulaiha Abubakar
June 25, 2020

Shugaban hukumar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock ya yi gargadin cewar idan kasar Yemen ta gaza samun wadatattun kudaden agaji nan bada jimawa ba, kasar za ta fuskanci durkushewa.

https://p.dw.com/p/3eIuX
Shugaban hukumar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, Mark Lowcock .
Shugaban Hukumar Taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, Mark Lowcock. Hoto: picture-alliance/Keystone/S. Di Nolfi

Matsananciyar yunwa da kuma yadda yara kanana suke kamuwa da cutar kwalara sakamakon rashin rigakafi a wannan lokaci da annobar COVID-19 ta karade kasashe, na haifar da asarar rayuka kowacce rana a kasar ta Yemen.

Mark Lowcock ya yi wannan gargadi ne a lokacin da ya ke yiwa Hukumar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniyar jawabi.

A farkon wannan wata na Yuni Majalisar Dinkin Duniyar da kasar Saudiyya suka jagoranci taro ta hanyar bidiyo na kaddamar da gidauniyar tallafin kudi ga kasar ta Yemen, to sai da har ya zuwa wannan lokaci alamu na nunar da cewar ba a kai ga cimma biyan bukata ba.