1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Saudiyya ta fara raguwa Yemen

Kersten Knipp HE/USU/LMJ
July 10, 2019

Mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa sun sanar da cewa za su janye dakarunsu daga rundunar taron dangin Saudiyya kasar Yemen, tare da daukar sulhu a matsayin matakin farko na kawo karshen rikicin kasar lakume rayuka.

https://p.dw.com/p/3LsA4
DW Exclusive Deutsche Waffen in Jemen SPERRFRIST 26.02.2019 20 Uhr VAE Soldaten Rückkehr
Sojojin Hadaddiyar Daular Larabawa na ficewa daga YemenHoto: picture-alliance/dpa/EPA/ENA

Tun dai a shekara ta 2015 ne Saudiyyan ta fara jagorantar rundunar taron dangin da Hadaddiyar Daular Larabawan ke taka muhimmiyar rawa a ciki, da nufin taimakawa gwamnatin Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi na Yemen din da al'ummomin kasa da kasa suka amince da ita, wajen yakar 'yan tawayen kungiyar Houthi da ake zargin Iran da mara musu baya. Sai dai har kawo yanzu ana iya cewa nasarar da suka samu ba ta kai ta kawo ba. Ana dai hasashen zai wahala a iya yakar 'yan tawayen na Huthi ta hanyar amfani da karfin soja, haka zalika 'yan ta'addan da ke tsibirin gefen kasar Yemen suma har yanzu suna nan. Ba abin da ake gani illa ci gaba da asararrayuka da dukiyoyin da kadarorin al'umma da gwamnati.

Ficewar Hadaddiyar Daular Larabawa daga yakin kasar ta Yemen dai, yazo a ba zata, ganin cewa dama baya ga Saudiyya kasar ce tafi karfin fada aji a yakin. Tuni ma dai mazauna jihar Marib a kasar ta Yemen suka sanar da cewa a yanzu babu alamar sojojin Hadaddiyar Daular Larabawan a jiharsu, da ke zama babban yankin da suka yi zango,. Hakama a jihar Hudaidai rahotanni sun nunar da cewa kawo dakarun da suka rage a yanzu ba su fi kaso daya bisa biyar na sojojin Hadaddiyar Daular Larabawan da ke yankin ba. Haka kuma a daya birnin mai tashar jiragen ruwa wato birnin Aden, 'yan kalilan ne daga sojojin Abu Dabi ake gani. Haka za lika sojojinsu da aka zube a kasar Eritiriya wandannda ke kai farmaki suma an yi matukar janyesu. 

Elizabeth Dickinson, jami'a ce a kungiyar kula da tashe-tashe hankula wato Suna gInternational Crisis Group, ta bayyana wasu daga dalilan da take ganin sun sa Hadaddiyar Daular Larabawan ficewa daga yakin na Yemen.

"Suna ganin yakin yana kara lakume kudinsu kuma suna asarar sojoji. Kasar ta dade tana neman mafita a rikicin musamman ta hanyar tattaunawar siyasa, abin da ya gaza samuwa. Ga kuma yanzu yadda yankin ke fuskantar zaman dar-dar. Ina ganin ba makawa tsarin siyasar yankin zai sauya cikin gaggawa. A ganina abu ne mai mahimmanci ga Hadaddiyar Daular Larabawa ta nemi warware yakin bisa zaman tattaunawa".

Sai dai a cewar Riad Kahwaji, Darakta a cibiyar tsarin sojojin yankin Gulf, ficewar Hadaddiyar Daular Larabawa daga yakin na Yemen, ba zai zamo abun ba zata ga kasar Saudiyya da ke jagorantar dakarun kawancen masu ruwan bama-bamai a Yemen din ba. A cewarsa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Duk da janye sojojin da Hadaddiyar Daular Larabawan ta yi, ba ta tsame hannunta daga yakin ba, domin kuwa ita ce za ta ci gaba da biyan sojojin kasar Sudan kimanin 10.000 wadanda za su ci gaba da zama a sansaninta da ke kasar Iritiriya. Hakama an bayyanan cewa sojojinta da ke sansanin Mukalla za su ci gaba da zama a matsayin shirin ko ta kwana.