Yemen: Annobar cutar kwalara ta yi kamari
July 23, 2017Talla
Kawo yanzu dai cutar ta kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da 800 a cewar Kungiyar ta CICR wadda kuma ta ce idan ba a yi hattara ba adadin wadanda za su kamu da cutar a wannan shekara ta 2017 zai kai na mutane dubu 600. Bincike ya nunar cewa cikin mutane 45 na kasar mutun daya na dauke da cutar ta kwalara a cewar kungiyar agajin cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce hakan kuma ba komai ba ne illa sakamakon yake-yaken da ya lalata muhimman gine-ginen kasar tare da durkusar da tsarin kiwon lafiya baki daya.