1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a tsagaita wuta a yakin Yemen

Abdourahamane Hassane
November 19, 2018

Wani jigo daga kungiyar 'yan tawaye na Houthi a kasar Yemen, ya ce a shirye suke su tsagaita bude wuta a yakin da suke yi da dakarun gwmnati karkashin jagorancin rundunar taron dangin da Saudiyya ke shugabanta.

https://p.dw.com/p/38Tzm
Jemen Konflikt
Hoto: Getty Images/AFP/M. Huwais

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da manzon musammun na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths zai kai ziyara kasar, domin shirya tattaunawa ta neman sulhu tsakanin bangarorin da ke yakin. Manzon na Majalisar Dinkin Duniya ya ce  gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya da kuma 'yan tawayen na Houthi wadanda ke samun goyan bayan Iran, sun nuna bukatar yin tattaunawar. Mutane kusan 10,000 ne suka mutu a yakin na Yemen da ake gwabzawa tun a shekara ta 2015 yayin da wasu dubbai suka arce daga kasar.