1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangaren Houthi sun gindaya sharudda kafin zaman lafiya

Ramatu Garba Baba
December 8, 2018

Wakilin 'yan tawayen Houthi Mohammed Abdusalam ya ce kafa gwamnatin riko da zai kunshi duk jam'iyyun siyasa zai iya tabbatar da shirin samar da zaman lafiya mai dorewa.

https://p.dw.com/p/39jLV
Jemen Waffenpause vor Friedensgesprächen in Genf Mohammed Abdul-Salam
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Abdusalam da ya wakilci 'yan Houthi a zaman sulhunta rikicin kasar na kusan shekaru hudu a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a Sweden, ya ce suna son a janye duk wasu jami'an tsaro da aka jibge a Hodeida da ke gabar teku, daya daga cikin wurare mafi mahinmanci da 'yan tawayen keda karfin iko. Abdulsalam ya ce Hodeida wuri ne da ake hada-hadar kasuwanci, ya dace a gudanar da harkokin kasuwancin cikin walwala inda duk 'yan kasa za su ci gajiyarsa. Mohammed Abdusalam ya tabo batutuwa da dama da za a yi la'akri da su kafin a sami daidaito.

Tun bayan soma yakin, dubban mutane sun rasa rayukansu yayin da mutane kimanin miliyan goma sha uku ke cikin tsanani na neman taimako, lamarin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce in har ba a dauki mataki magancenta, akwai yiyuwar ta janyo yunwa mafi muni da aka taba yi cikin shekaru dari.