1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kai mayakan Houthi asibiti

Ramatu Garba Baba
December 3, 2018

A wannan Litinin aka shirya kwashe wasu mayakan Houthi akalla 50 da suka sami rauni a yayin wani gumurzu zuwa wani asibiti da ke birnin Muscat bisa yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna.

https://p.dw.com/p/39Ird
Jemen Konflikt - UN-Flugzeug - Hilfe
Hoto: picture alliance / dpa

A wannan Litinin jirgin Majalisar Dinkin Duniya zai kwashi majinyatan zuwa birnin na Muscat, bayan da mayakan Houthi suka bayar da tabbacin bayar da hadin kai muddun aka biya musu wannan bukata a batun da za a iya cewa ya mayar da hannun agogo baya, a yunkurin da aka sha yi don ganin an sulhunta rikicin da ya lakume dubban rayuka.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Yemen, Martin Griffiths ya yaba da matakin da ya ce alama ce, ta nuna yarda da juna da ake bukata a wannan lokaci. Majalisar na ci gaba da yin gargadi kan daukar matakin kaucewa bala'i na yunwa da ka iya afkawa Yemen muddun aka gagari shawo kan rikicin. A wannan makon ake sa ran zaman taro kan rikicin a kasar Sweden.