Yawon bude ido a gandun namun dajin Afirka
Gandun daji fiye da 300 ake da su a sassan kasashen nahiyar Afirka inda ake ajiye namun daji dabam-dabam, ga wasu daga cikin dabbobin masu ban sha'awa da jama'a ke tururuwa don yin tozali da su.
Gandun dajin Serengeti na kasar Tanzaniya
Gandun dajin na da tsawon kusan kilomita 5,000, ya kasance daya daga cikin gadun dajin mafi girma da ya shahara a duniya. Abin dubawa shi ne, babu inda aka taba samun namun daji da ke son kaura kamar yadda lamarin ya ke a dajin. Da zarar an shiga damina a watan Maris da Afrilu, miliyoyin dabbobi da suka hada da jakin dawa da barewa suna kaura zuwa yankin arewacin kasar.
Gandun dajin Amboseli na kasar Kenya
Abin alfahari ga kasar Kenya da ke da akalla gandun daji 23 amma gandun dajin na Amboseli shi ya fi yin fice. Ya kasance a karkashin yankin da ake da tsaunin Kilmanjaro wato tsauni mafi tsayi a Afirka. Ya shahara bisa tarin giwaye da ke ciki inda aka kebe su daga barazanar mafarauta namun daji. 'Yan kabilar Massai da ke rayuwa a yankin suna aiki tukuru don kare rayuwar giwayen.
Wurin shakatawa na Sarauniya Elizabeth a Yuganda
Masu yawon bude ido na son shakatawa a wannan wuri, ganin yadda suke iya hangen kasar daga wannan wuri na saukar baki daga kololuwa. Tamkar an tsara wurin ne don bai wa jama'a jin dadin yanayi ta hanyar nishadi inda suke iya kallon hikimar rayuwar mutum da kuma namun daji. Wuri ne na musamman a yankin kahon Afirka da ke baiyana ni'ima da albarkatun kasa.
Gandun dajin Volcanoes na Ruwanda
Ana da nau'o'I dabam-dabam na gwaggon biri akalla 12 da ke rayuwa a tsaunukan Virunga. Masaniya kimiyyar dabbobi Dian Fosse ce ta soma baiyana wa duniya na'u'in biran. Ta zauna a cikinsu inda a nan ta gano rashin illar gwaggon biri kuma tun wancan lokaci ake samun masu yawon bude ido da ke ci gaba da yin tozali da dabbar ba tare da fargaba ba amma sai da rakiyar mafarauta da aka yi wa horo.
Gandun dajin Kruger a Afirka Ta Kudu
Babu abin da masu yawon bude ido ke sha'awar gani a nahiyar Afirka kamar gamaiyar dabbobi da suka hada da zaki da giwa da karkanda, da baunar Afirka da kuma damisa. A yayin yawon kewaye gandun dajin Kruger, akwai damar yin tozali da zakoki, inda ake da sama da dubu daya da dari biyar. Wasu don shakatawa su kan kewaye gandun dajin da tafiyar kafa.
Victoria Falls na kasar Zimbabuwe
Wani yanki ne da ke karkashin kulawar UNESCO tun daga shekarar 1989. Victoria Falls na a tsakanin kan iyakar kasar ta Zimbabuwe da kasar Zambiya, Yana daya daga cikin tsaunuka da ruwa ke kwarara a duniya. Ruwan na kwararowa inda yake mamaye fadin akalla mita 1,700. Kasada ce yunkurin yin ninkaya a Victoria Falls.
Gandun Sanganeb Marine na kasar Sudan
Masu sha'awar yin ninkaya daga sassan duniya na matukar son zuwa wannan wurin shakatawar da ke gabar ruwan kasar ta Sudan. A tekun Bahar Maliya, ana iya ganin giwayen ruwa da kifin Dolphins da ma wasu na'u'in kifaye da ke cikin tekun. Wurin ya kasance karkashin kulawar hukumar UNESCO tun daga shekarar 2016.
Gandun Tassili n’Ajjer na kasar Aljeriya
Wuri ne da ake da manyan duwatsu masu cike da al'ajabi.Tassili n’Ajjer ya zarta har zuwa yankin Sahara. Tun daga shekarar 1950 aka gano wasu duwatsu na sama da shekaru dubu 10. Yanki ne da ake samun makiyaya 'yan kabilar Tuareg. Makiyayan sun shahara a iya karrama baki, ana cewa duk wanda ya zauna da su har ya sha kofin shayi uku da su, to ko shakka babu za su ba shi kariya ta musamman.
Gandun Namib-Naukluft na kasar Namibiya
Gandun da ke a yankin Namib, ya kasance mafi dadewa a tarihin duniya. Rakuma sun yi sanadiyyar kashe bishiyoyin da ke cikin gandun dajin, sai dai an yi nasarar kebe su da kuma ba su kulawa ta musamman duk da matsalolin daga matsalar sauyin yanayi. Ana iya hawa kololuwa gandun inda wasu ke wasan rikitowa daga samansa don burgewa.