Gwamnati da kungiyoyin 'yan tawayen Sudan sun rattaba hannu
August 30, 2020Talla
An bayyana cewa Firaminista Abdallah Hamdok na Sudan da wasu mukrabban gwamnatin rikon kwarya suka isa a birnin Juba, inda suka gana da shugaba Salva Kiir na Sudan Ta Kudu, kafin ranar Litinin inda daukacinsu da sauran jiga-jigan kungiyar FRS ta 'yan yakin sunkurun kudancin Sudan za su halarci bikin rattaba hannu da gwamnati.
Wannan dai na a matsayin wata matattakalar wanzar da zaman lafiya tsakanin 'yan kasar Sudan a cewar Firaminista Hamdok.