Kasar Yemen na ci gaba da shiga halin tasku
October 21, 2015Talla
UNICEF din ta kara da cewa matsalar za ta haifar da rashin abinci mai gina jiki da kuma cututtuka ga kananan yaran 'yan kasa da shekaru biyar a kasar. Kawo yanzu dai sama da mutane 5,500 ne suka hallaka tun bayan da Saudiya ta kaddamar da kai hare-hare ta sama tare da tallafin sauran kawayenta kasashen Larabawa a Yemen din. Cikin watan Maris din da ya gabata ne dai Saudiyan ta fara jagorantar rundunar taron dangin kasashen Larbawan wajen kai wa ksar ta Yemen da ke fama da dunbin talauci hare-hare ta sama, a wani mataki da ta kira da kokarin fatattakar 'yan tawayen Houthi da ke zaman Musulmi mabiya shi'a wadanda suka kwace iko da babban birnin kasar Sanaa.