'Yancin mata da daidaituwar al'amura
March 11, 2019Talla
Shirin na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ranar mata ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware kuma ake gudanar da bikin a ranar takwas ga watan Maris na kowacce shekera. Shirin dai ya ji ta bakin matan su da kansu da kuma kungiyoyin da ke rajin kare hakkin mata. Taken bikin na wannan shekarar dai shi ne "Daidato domin samun ci-gaba".
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shin me kungiyoyin da ke rajin kare hakkin mata ke yi domin wayar da kan matan kan hakokinsu da kuma 'yancin da suke da shi?
Shin su kansu matan sun san cewa akwai wata rana da Majalisar Dinkin Duniya ta ware da zummar yin bukukuwa domin 'yancinsu?
Wadannan tambayoyi ne dai shirin na wannan lokaci zai amsa.