Talla
A ranar Talata (08.11.2016) ce aka bude rumfunan zabe don zaben shugaban kasa na 45 a Amirka inda takara ta fi zafi tsakanin Hillary Clinton ta jam'iyyar Demokrat da Donald Trump na jam'iyyar Demokrat. Bisa al'ada hukumomi kan fidda tsare-tsare da kuma yanayi na zaben gama-gari a kasar ta Amirka kamar yadda ke kunshe cikin wannan rahoton da wakilinmu da ke Washington Kabir Isa Jikamshi ya aiko mana.